Monday, December 21, 2009

Sardaunan Kano Ya Wallafa Littafin Salati Ga Annabi S.A.W

Bangon Littafin Salati Ga Annabi S.A.W Da Sardaunan Siyasa Ya Rubuta.

Sardaunan Siyasa Ne Mai Akidar Sardaunan Kano

Sardaunan Siyasa A Yayn Da Ya Waklci Sardaunan Kano Domin Karbar Masa Lambar Yabo Da A Ka Bashi A Kasar Malesiya

Ba A Zama Sarkin Dawa Sai An Gagari Zaki

Kamar yadda Hajiya Binta Sayyadi ta tabbatar a jawabinta na jadda cewar kwamishinan Muhalli Garba Yusif Abubakar ne mai akidar Malam. Ko kadan bata yi kuskure ba. Domin binciken da na gudanar dangane da masu akidar Malam masana sun tabbatar min cewar shine kadai a gwamnatin Malam day a hada wadannan siffofi na sa. Ga kadan daga ciki kamar haka:
Koyar da karatu a gidansa na Kwalli kafin ya shiga siyasa. Yana koyar da karatu a Kankarofi inda ake yiwa laAkbi da fanfom yari daga mariba zuwa isha. A women Centre ya kafa makarantar mata mai suna Ummus-Salama. Yana daya daga cikin jigon kafa makarantar gidan Makama mai suna Nana Aisha. Shine sakataren kudi a kungiyar daliban musulmai da ake yiwa lakabi da Muslim student society. A kasa kuma jami'in hulda da jama'a. Kuma shine madugu uban tafiya a cibiyar tabbatar da hadin kai tsakanin addinai mai suna Centre For Islamic Co-Existance. Yana bin makarantun maza da mata yana fadakarwa. Yana kuma yawaita halartar wajen saukar karatun Alkur'ani.
Zurfin addini ta inda duk abinda zai fada sai ya danganta shi da Nafsin Alkur'ani ko Hadisi. Zurfin Imani da fauwala dukkan lamari ga Ubangiji. Kyakkyawar alaka da mutane. Ganin girman mutum komai kankantarsa. Sanin hakkin jama'a. Taimakon al'umma ba tare da sanya riya a ciki ba. Buga tarin littattafai na musulunci a harshen Hausa da Turanci. Kadan daga ciki su ne kamar haka: Islam And Cristianity: Peace or violence? God is not an author of confusion. The unity of God. Globalization. The receipt of co-existance. Leadership.
Iya dadadan kalamai masu sanyaya jiki da gamsarwa ga mai sauraro. Shine mai warware matsalar siyasa yayin da tarnaki ya turnuko. Misali lokacin da aka samu rashin fahimtar juna tsakanin malaman makarantun gaba da sakandire da gwamnatin jiha, shine ya shiga ya warware wannan rikici aka samu daidaito. Kuma a lokacin da sashin Hausa na Amirka suka saki muryar Malam akan janar Buhari, shine kadai ya iya fitowa kafar yada labarai ya kwantar da wannan kura.
Yana cikin kungiyoyin addinin musulunci da dama masu gudanar da lakcoci da musuluntar da maguzawa. Ga kuma halartar majalisu na addini ba tare da gajiyawa ba. Kuma shine mai yawan wakiltar Malam a yayin muhimman abubuwan da uzuri ya han shi zuwa. Ko digirin girmamawa da aka bawa Malam a kasar Malesiya da bai samu damar zuwa ba. Alhaji Garba Yusif Abubakar ne ya wakilce shi, ya kuma karba a madadinsa.

Himma Ba Ta Ga Rago

Sardaunan Siyasa na Karbar Lambar Girmama A kan Kimiyyar Muhalli
Sardaunan Siyasa Na Karbar Lambar Yabo Daga Magada Annabawa

Mutum Na Mutane Mai Sauraron Mutane


Sardaunan Siyasa Ne Shugaban Kwamitin Bikin Nadin Sardaunan Kano


Kwamishinan muhall kuma Sardaunan Siyasa Malam Garba Yusif Abubakar aka nada matsayin shugaban kwamitin bikin nadin sarautar Sardaunan Kano gwamna Malam Ibrahim Shekarau. Wanda za a gabatar a watan Janairun sabuwar shekarar 2010.